Babu wata kasa daya da za ta ci gaba ba tare da sanin makamar aiki ba, musamman ta fuskar inganta harkar sa ido tare da samar da kwarin gwiwa ga matasa.
Alfijir Labarai ta rawaito Mataimakin gwamnan, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi rahoton kwamitin farfado da cibiyoyin koyar da sana’o’i na jiha karkashin jagorancin Farfesa Aminu Suleman, a ofishinsa a yau.
Kwamared Abdusalam Gwarzo, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake ruguza cibiyoyin koyon sana’o’i da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar a lokacin mulkinsa da nufin karfafawa matasa da ba su da damar samun digiri ko na biyu, yana mai jaddada cewa baya ga gwamnatin Jihar Jigawa, Kano. Jiha ce ta biyu da ta samar da Informatic institute a kasar nan a lokacin.
Ya kuma tabbatar da aniyar gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf, domin farfado da dukkan cibiyoyin koyon sana’o’i a jihar domin ci gaban matasa masu tasowa ta yadda za su zama masu dogaro da kai.
“Mun dawowa ne bayan an kwashe shekaru masu yawa, mun baiwa al’ummar jihar tabbacin cewa mai girma gwamna Engr Abba Kabir zai farfado da cibiyoyin, in ji Kwamared.
Ya godewa kwamitin bisa aikin da suka yi, sannan ya yabawa Hon. Kwamishinan ilimi mai zurfi, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar mata bisa hangen nesan sa na kafa kwamitin da kuma kammala aikin a cikin wa’adin.
Tun da farko shugaban cibiyar farfado da cibiyoyin koyar da sana’o’i, Farfesa Aminu Suleman ya ce domin a gano abubuwan da ake da su.
Matsayin cibiyoyin da kuma gazawarsu tare da gabatar da rahoton rubost, hanyoyin da kwamitin zai gudanar da aikinsu yadda ya kamata da kuma samun nasara.
Farfesa Aminu, ya bayyana cewa bayan duba wuraren aikin kwamitin ya fito da sakamakon bincikensu da shawarwarin da za a ci gaba da aiwatarwa,
Shugaban ya kuma godewa gwamnatin jihar da ta ba su damar yi wa jiharsu hidima domin amfanar al’umma.
Shima da yake jawabi, Hon. Kwamishinan ilimi mai zurfi Dr. Yusuf Ibrahim Kofar mata ya yabawa gwamnatin jiha karkashin ingantacciyar jagorancin gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf saboda damuwarsa ta sake farfado da cibiyoyi masu dumbin yawa.
Kamar yadda Sunusi KofarNaisa, babban Jami’in Yada Labarai na matakin Gwamnan Jihar Kano.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb