Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta raufe rassan bankin UBA kan kin biyan harajin Naira miliyan 14.
Alfijir Labarai ta rawaito KADIRS ta rufe rassan bankin guda shida da ke Kaduna ne bayan hukumar gudanarwar bankin ya gaza biyan harajin da ake bin su, duk da takardun tunatarwar da hukumar aike musu a lokuta daban-daban.
Sakataren Majilisar Gudanarwar kuma Mai ba da Shawara kan Shari’a ta KADIRS, Barista Aysha Muhammad da rakiyar jami’an tsaro ta jagoranci rufe rassan bankin.
A cewarta, hukumar ta dauki matakin ne da nufin karbo bashin kudaden haraji Naira N14,367,322.20k da suke bin bankin daga shekarar 2019 zuwa 2021, kamar yadda dokar hukumar ta tanadar.
RN
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk
