Ba Ma Son Yaƙi Amma Mun Shirya Zamu Kare Kasar Mu Idan Hakan Ta Faru

Yan tawaye ba sa neman karbe madafun iko a kasar sai dai suna neman a cimma matsaya da za ta dace da muradun jama’a.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban sojojin da suka kwace mulki a Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya fada a ranar Asabar cewa kasarsa ba ta son yaki, amma za ta kasance a shirye don ta kare kanta idan hakan ta faru.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta nakalto Mista Tchiani yana cewa “Sojoji ko al’ummar Nijar ba sa son yaki, amma za mu yi tir da duk wata alama ta sa.”

Ya kuma yi nuni da cewa, kasashe mambobin kungiyar ECOWAS, ba su fahimci cewa Nijar ta zama mabudin dakile tashe-tashen hankula a yankin ba sakamakon karuwar ayyukan ta’addanci.

Mista Tchiani ya kara da cewa takunkumin da aka kakaba wa kasarsa na nufin matsin lamba ne a kan ‘yan tawaye, ba wai don nemo mafita kan halin da ake ciki a yanzu ba.

Bugu da kari, Mr Tchiani ya ce ‘yan tawaye ba sa neman karbe madafun iko a kasar sai dai suna neman a cimma matsaya da za ta dace da muradun jama’a.

A ranar Asabar din da ta gabata ne kafafen yada labarai suka rawaito cewa tawagar ECOWAS ta isa babban birnin Nijar inda ta gana da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum domin tantance yanayin tsare shi, tawagar ta kuma tattauna da Mista Tchiani.

Bayan juyin mulkin, ECOWAS ta dakatar da duk wani tallafin kudi da take baiwa Nijar, tare da dakile kadarorin ‘yan tawaye, tare da sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci zuwa kasar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *