APC Za Ta ƙarbe Jihar Kano A Kotu Daga Hannun NNPP Bada Jimawa Ba – Sanata Barau

Muna addu’a kuma muna fatan sakamakon kotun ya yi mana kyau.

Alfijir Labarai ta rawaito Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya ce jam’iyyar APC za ta kwato jihar Kano a kotu daga hannun jam’iyyar (NNPP). Nan bada jimawa ba.

Jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin Rabi’u Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, ta lashe kujerar gwamna da kujerun sanatoci biyu a jihar a lokacin babban zabe, yayin da Barau, dan takarar jam’iyyar APC ya samu kujerar Sanata na uku.

A halin yanzu dai jam’iyyar APC a Kano tana kotun sauraron kararrakin zabe tana kalubalantar nasarar Abba Yusuf, gwamnan jihar mai ci.

Da yake magana a lokacin da tawagar mataimakan shugabannin kananan hukumomi (ALGOVC) a Kano suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja ranar Laraba, Sanatan ya ce yana da kwarin gwiwar cewa kotun za ta yanke hukunci a kan APC.

“Komai yana hannun Allah. Mu hada kai mu yi aiki tare. In sha Allahu lokaci ya yi, za mu koma jihar Kano.

“Kamar yadda yake a yanzu, muna cikin ‘yan adawa kuma don haka akwai fata da yawa daga gare mu. Kamata ya yi mu hada kai,i domin cin moriyar jam’iyyarmu.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

One Reply to “APC Za Ta ƙarbe Jihar Kano A Kotu Daga Hannun NNPP Bada Jimawa Ba – Sanata Barau”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *