Akwai yiwuwar kamfanoni sadarwa za su ƙara kuɗin kira da na data da kuma tura rubutaccen saƙo a farkon shekarar 2025 mai kamawa.
Alfijir labarai ta rawaito wani babban jami’in wani kamfanin da sadarwa ya bayyana cewa kamfanonin suna da ƙwarin gwiwar samun sahalewar Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) domin kara kuɗin kira da na data.
Jami’in wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa kamfanonin sadarwar na MTN da Airtel da 9Mobile sun riga sun aika wa NCC da buƙatarsu kuma bisa dukkan alamu suna ganin haske.
Burinsu hukumar NCC ta amince da burinsu na ƙarin kuɗin da suka shafe kusan shekara goma suna nema, ta biya ke nan.
Hukumar NCC ta ƙi amince wa kamfanonin ƙara kuɗi tun a zamanin tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami.
Kimanin shekara 10 ke nan yanzu kamfanonin suke neman ƙara kuɗi kira da na data da tura saƙonni, bisa dalilin hauhawar farashin kayayyaki, amma gwamnati tana ƙin ba su damar yin hakan.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj