An Yiwa Lai Mohammed Sabon Mukami A Majalisar Dinkin Duniya

Tsohon ministan Buhari, Alhaji Lai Mohammed, ya sami sabon aiki da majalisar dinkin duniya, in da sakataren na majalisar kan harkokin yawon bude ido “United Nations World Tourism Organisation” Mista Zurab Pololikashvili, ya nada shi a mastayin mai bashi shawara.

A cikin wata sanarwa da aka bawa kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN, ta nuna cewa an sanar da bawa Lai Mohammed mukamin ne a wajan wani taro da majalisar take gudanarwa a Mauritius.

Ya yin da yake karbar mukamin, Mohammed ya yi godiya ga sakataren bisa bashi wannan mukami da akai, kuma ya yi alkawarin zage danste don ganin ya yi abinda ake tsamma ni daga gareshi.

“Naji dadin wannan mukami da mai girma Zurab Pololikashvili ya bani, kuma zan yi iya kokarina wajan gudanar da aikina yadda ya kamata.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *