An Yanka Ta Tashi: Wasu tsoffin ƴan majalisa  sun yi watsi da goyan bayan takarar Tinubu a 2027

IMG 150604 10625 1749564376482

Aƙalla tsofaffin ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa 17 sun nesanta kansu daga wani taron da aka ce tsofaffin ‘yan majalisa sun shirya domin amincewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan burinsa na wa’adi na biyu.

A wata sanarwa ta haɗin gwiwa da suka fitar a ranar Asabar, tsofaffin ‘yan majalisar sun ce ba su halarci wani taro ƙarƙashin sunan Ƙungiyar Tsofaffin ‘Yan Majalisa (NFFL) ba, kuma sun bayyana cewa amincewar da aka yi tana cike da ruɗani da yaudara.

Sun yi zargin cewa taron da aka gudanar, wanda shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya shirya, an yi shi ne don neman kuɗi, ba bisa  wakilcin ra’ayin tsofaffin ‘yan majalisa ba.

Tsofaffin ‘yan majalisar sun jaddada cewa ba za a yi amfani da sunayensu ko martabarsu ba tare da izini ba, suna mai cewa su ba kayan sayarwa ba ne a harkar siyasa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito kungiyar ta sanar da cikakken nesanta kanta daga taron da kuma duk wata sanarwar goyon baya da aka fitar da sunanta, tana mai Allah wadai da abin da ta kira sayar da darajar dimokiraɗiyyar Najeriya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *