An Kama Ɗan Takarar Shugaban Kasa Peter Obi A London

Alfijr ta rawaito an tsare dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi a Landan, kasar Birtaniya inda ya je bikin Easter, kakakin kamfen din Obi-Datti, iran Onifade, ya bayyana.

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu, Onifade ya kuma bayyana cewa jami’an hukumar kula da shige da fice na Landan sun ci zarafin Obi sannan suka tsare shi, kamar yadda  Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, Obi ya isa filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan daga Najeriya a ranar Juma’a, 7 ga watan Afrilu sannan ya bi layi don cike ka’idojin filin jirgin saman lokacin da jami’an suka kwamashe shi sannan suka nemi yayi gefe.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *