
Alfijr ta rawaito majiya mai tushe ta bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Anambra Dr Chinwoke Mbadinuju ya rasu a asibitin Abuja.
Dan marigayin, Cheta, ya ce Mahaifin nasu ya rasu ne a ranar Asabar a babban asibitin kasa, Abuja yana da shekaru 78.
Cheta ya sanar da rasuwar a madadin Iyalan marigayin a wata sanarwa da ya fitar a Awka kuma ya mika wa manema labarai a ranar Talata.
Ya ce: muna sanar da rasuwar mahaifinmu, kakanmu, kawunmu, abokinmu kuma abokin tarayya, Dokta Chinwoke Mbadinuju, tsohon gwamnan Anambra, kuma dattijon jihar.
Ya Kara da cewa ” Muna addu’ar Allah ya jikansa da rahamarsa da wadanda ya bari domin yi masa makoki.
Cheta ya kara da cewa “iyali za su sanar da shirye-shiryen jana’izarsa nan gaba kadan.”
A nasa jawabin, Gwamna Chukwuma Soludo ya jajantawa iyalan mamacin da al’ummar Uli ta karamar hukumar Ihiala da daukacin al’ummar Anambra bisa wannan rashi.

A cikin wata sanarwa da Christian Aburime ya sanya wa hannu, Sakataren yada labaransa, Soludo ya ce marigayi ‘Odera’, kamar yadda aka yi masa kirari da jin dadi, za a iya tunawa da shi da sanya hannu a kan dokar da ta kafa ma’aikatar Vigilance ta Anambra, Jami’ar Jihar Anambra, Uli, da dai sauransu.
Ya kuma bukaci ’yan uwa da su tabbatar da dorewar kyawawan abubuwan gadonsa, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama.
Mbadinuju ya kasance gwamnan Anambra daga 1999 zuwa 2003.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ