Alfijr ta rawaito Jami’an ƴan sanda sun gurfanar da matashin a gaban kotun mai shari’a Nura Yusuf Ahmad, da ke unguwar Gama PRP a bisa tuhumar tsoratarwa.
Mai gabatar da karar, Aliyul ‘Abidin, ya shaida wa kotun cewa budurwar ta janye sakamakon wanda ta shigar da karar a kansa saurayinta ne.
An zargi matashin da yunkurin bata wa budurwa suna, bayan ya yi mata barazanar yada hoton tsiraicinta a Facebook, wanda hakan na iya bata mata suna.
Tun da farko saurayin ya yi wa budurwar barazana ne domin ta saya masa waya.
Sai dai bayan janye kararta, kotun ta sallami matashin da ake tuhuma, inda ta gargade shi kan yi wa mutum barazana.
Barazana yada hoton tsiraicin ’yan mata a kafafen sada zumunta lamari ne da ke yaduwa kamar wutar daji yanzu haka, sai muce kowa ya yi nagari!
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇