An gano Yaro dan shekara 17, bayan shafe shekaru biyu yana amfani da sunan dan Gidan Gwamnan Kano domin damfara
Wani Yaro dan shekara 17 mai suna Abdulbasi Aminu, dan unguwar Hausawa Zoo Road dake ƙaramar hukumar Tarauni a Jihar Kano, ya shiga komar hukumar yaki da rashawa da karbar korafe-korafen al’umma ta Jihar Kano, bisa laifin amfani da sunan dan Gidan Gwamnan Kano, Al-Ameen Abba Kabir Yusuf, wajen damfarar mutane, da kuma wasu laifuffuka da suka hada da bayyana kansa a matsayin Jami’in Gwamnatin Kano.
Tunda fari dai shugaban ƙungiyar masu dakkowa Gwamnan Kano rahoto na musamman, Amir Abdullahi Kima, tare da babban mai taimakawa Gwamnan Kano a kafafen sadarwar zamani, Salisu Yahaya Hotoro, ne suka shigar da korafi zuwa ga hukumar, inda aka shafe wasu kwanaki ana gudanar da bincike.
Yaron ya bayyana sunayen wadanda yake amfani dasu wajen yin wannan ayukka nasa, amma daga bisani an cimma matsaya akan karyata kansa bisa wadancan tuhume-tuhume da kuma da tabbatar da daina cigaba da aikata wadannan laifuka.
Daga cikin abubuwan da aka samu yaron dasu sun hada da, buga jabun takardar tafiye-tafiye (Visa), jabun kudin Dollar, da jabun sakon tura kudi (fake alert), da kuma jabun ID card din Gwamnati da yake karbar kudaden Yara domin ya samu ID card.
Hakazalika an same shi da laifin yin amfani da sunan Al-Ameen Abba Kabir Yusuf wajen yin kyautar kujerar aikin Hajji ga wasu masu kwaikwayon Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Alhaji Abba Kabir Yusuf da kuma Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, da sauran wasu yara inda daga baya aka gano ba gaskiya bane.

Kwankwasiyya Reporters
Ga Masu Son Bada Talla A Kira +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN