An Fara Tattara Sakamakon Zaɓen Da Aka Gudanar A Kano

Alfijr ta rawaito An kammala kada kuri’a a rumfunan zabe 206 a kananan hukumomi 15 na jihar Kano inda aka sake zaben ranar Asabar.

A yayin da wakilan jam’iyya, masu sa ido kan zabe, da sauran hukumomi ke bin diddigin yadda ake gudanar da ayyukan a cibiyoyin tattara sakamakon zabe daban-daban na jihar domin tabbatar da gaskiya.

An kuma kara daukar matakan tsaro a kokarin tabbatar da tattara sakamakon zabe cikin lumana.

Tun da farko dai duk da dokar hana zirga-zirga a jihar da ‘yan sanda suka yi, an ga motsin ababen hawa a yayin da ake gudanar da zaben.

Kano na da zabukan mazabar tarayya guda biyu da na ‘yan majalisar jiha 14.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *