Mamba mai wakiltar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam, Yusuf Gagdi, ya baiwa ƴarsa kyautar dalleliyar mota kirar Lexus RX, crossover SUV, domin murnar kammala karatun sakandire tare da samun maki mai kyau a jarrabawarta ta shiga jami’a, UTME.
Alfijir labarai ta ruwaito Ƴar ta sa mai suna Aisha Gadgi ta kammala karatunta a makarantar Lead British International School Abuja a jiya Asabar.
Wani shahararre a Facebook, Saminu Maigoro, ya wallafa hotunan matashiyar tare da mahaifinta, suna baje kolin motar ta alfarma.
“Ina taya Aisha Yusuf Gagdi murnar kammala karatunki a makarantar Lead British International School Abuja. Allah Ya sa hakan ya zama mafarin ci gaban ki a rayuwa.
“Don murnar kammala karatun ta da kuma rawar da ta taka a JAMB, mahaifinta ya ba ta mamaki da kyautar mota,” in ji Mista Maigoro.
Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta lura cewa kyautar ta janyo cecekue a shafukan sadarwa, inda wasu su ke goyon bayan hakan, wasu kuma su ke alla-wadai duba da matsin rayuwa da ƴan Nijeriya ke ciki.
Daily Nigerian
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj