Alfijr ta rawaito Alkalan kotun daukaka kara ya mutu a cikin kotun lokacin shari’ar rana.
Mai shari’a Lokulo-Sodipe har zuwa rasuwarsa yana daya daga cikin alkalai a kotun daukaka kara da ke Akure.
An rantsar da shi ne a ranar 15 ga watan Fabrairun 2008 kuma ya yi aiki a sassan Abuja, Enugu da Benin har zuwa Afrilu 2014, lokacin da aka tura shi mukamin da yake yi a yanzu a sashin Ekiti.
Daga cikin mukamai da dama da ya rike, ya kasance dan Majalisar Dokokin Jihar Anambra da Kuros Riba a shekarar 1999, sannan ya kasance dan Majalisar Dokoki ta kasa, Gwamna da na ‘Yan Majalisun Dokoki na Kasa, na Kotun sauraren kararrakin zabe na Jihar Benuwe a 2003.
Shugaban kwamitin bayar da rahoto na shari’a na jihar Ogun daga Disamba, 2001 zuwa Janairu, 2008.
Hon. Mai shari’a Lokulo-Sodipe ya auri Misis Afolake Ibironke Lokulo-Sodipe kuma ta haifi ‘ya’ya biyu.
Marigayin dan asalin Abeokuta ta Kudu ne a Jihar Ogun, kuma an kira shi Lauyan Najeriya a shekarar 1979.
Ana yi masa kallon alkali mai himma kuma ƙwararren marubucin hukunci.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇