Aƙalla Yara almajirai 11 sun mutu bayan da rami ya rufta da su a Kaduna

IMG 175817 04625 1749056320491

Aƙalla yara goma sha ɗaya ne suka rasa rayukansu a jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya bayan wani tarin yashi ya rufta kansu yayin da suke tono laka daga rami.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen ‘Yardoka da ke yankin Kubau a ranar Litinin, kamar yadda kafofin watsa labarai na cikin gida suka ruwaito.

Yaran da suka mutu almajirai ne, masu shekaru tsakanin 10 zuwa goma 15, waɗanda aka ce malaminsu ya tura su domin su samo laka don yin tubalin kasa.

Yara bakwai kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawa saboda raunukan da suka samu.

“Tara daga cikin waɗanda suka mutu ba mazauna Yardoka ba ne, amma almajirai ne da suka zo tare da malaminsu domin karatu.
“Ba suna yin tubalin don sayarwa ba ne; wannan wurin dai ana amfani da shi ne a ƙauyen wajen tono yashi idan ana gini ko gyaran gidaje,” kamar yadda wani dagaci ya shaida wa jaridar Daily Trust ta Nijeriya.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya shaida wa kafofin watsa labarai na cikin gida cewa jami’an tsaro sun isa wurin da abin ya faru nan take bayan samun kiran gaggawa. Hukumomi sun fara bincike kan lamarin.

Rufewar ramukan yashi da ke haifar da mutuwar mutane ba sabon abu ba ne a Nijeriya. Sai dai, ƙasar da ke da albarkatun ma’adanai ta sha fama da ruftawar ma’adinai a cikin shekarun baya bayan nan.

TRT Hausa

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *