Ibtila’i : ‘Yar Majalisar Dattawa Ta Farko A Najeriya Ta Rasu Tana Da Shekaru 79

Alfijr ta rawaito Franca Afegbua ta rasu tana da shekaru saba’in da tara.

A cewar wata majiya mai tushe, Afegbua ya rasu ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Maris, 2023.

“Iyalan Afegbua na jihar Edo sun tabbatar da rasuwar mace ta farko a majalisar dattawa a Najeriya, Sanata Franca Afegbua, wanda lamarin ya faru a safiyar yau Lahadi, 12 ga watan Maris 2023.

Iyalin za su sanar da bayanan jana’izar nan ba da jimawa ba,” in ji dangin.

Cif Afegbua daga gudanar da wani salon gyaran gashi a Legas, ta lashe gasar gyaran gashi ta duniya da aka yi a Landan, Cif Afegbua ta kafa tarihi a lokacin da ta tsaya takarar Sanatan Bendel-North a zaben 1983.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *