NDLEA Ta Kama Tubabben Ɗan Boko Haram Da Wani Basarake Bisa Safarar Kwayoyi

Alfijr ta rawaito Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama wani tsohon mayakin kungiyar ta’adda ta Boko Haram, Alayi Madu da kuma mai rike da sarautar gargajiya, Baale Akinola Adebayo bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a yau Lahadi a Abuja

Babafemi ya ce an kama basaraken ne a garin Kajola da ke kan iyaka da jihar Ondo da Edo.

Ya kuma ce da sanyin safiyar Juma’a, 10 ga watan Maris, jami’an hukumar NDLEA sun kai farmaki dajin Kajola da ke unguwar Kajola, da ke kan iyaka tsakanin jihar Edo da Ondo, inda suka lalata gonakin tabar wiwi guda uku, wanda girman ya kai hekta 39.801546.

“An kama mai gonakin da ke ikirarin shi Ba’ale na Kajola, Akinola Adebayo, mai shekaru 35, a gonar da karfe 2:30 na safe.

“Wasu mutane biyu da ake zargin ma’aikatansa ne: Arikuyeri Abdulrahman, mai shekaru 23 da Habibu Ologun, mai shekaru 25, su ma kama su a wata bukka da ke kusa da gonakin.

“Haka kuma, wani Alayi Madu mai shekaru 26, wanda ya kasance mayakin Boko Haram na tsawon shekaru 15 kafin ya mika wuya ga sojojin Najeriya a 2021, jami’an NDLEA sun kama shi.”

Mista Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin a hanyar Abuja-Kaduna a ranar Alhamis ɗauke da kilo 10 na kwayar skunk.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *