Matawalle Ya Bada Umurnin Kama Duk Wani Wanda Yaki Karbar Tsohon Kudi

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Alfijr ta rawaito Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Bello Muhammad Matawalle ta bada Umurnin Kama Duk wani wanda yaki karbar tsohon kudi .

Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin taron rantsar da masu bashi shawara daya gudana a gidan gwamnatin Jihar.

Ya Kara da cewa suna sane da halin da talakawa suke ciki Kan matsalar canjin kudi, hakan ya sanya suka hada kansu su uku , shi da gwamnan Jihar Kaduna da koyi suka kai gwamnatin taraiya kara kotu.

Ya Kara da cewa haka yasanya kotu ta da katar da Babban Bankin kasa CBN da kin karbar tsaffin kudade har sai zuwa Sha Biyar ga watan biyu 2023.

Bello ya ce saboda haka Jama’a suci gaba da amfani da kudadensu duk Kuma wanda yaki amsar Tsohon kudi to a kai karanshi ga Jami’an tsaro.

Gwamnan yace ya gana da manajojin bankunan da ke jihar zamfara, Kuma ya umur cesu dasu ci gaba da amsar kudaden Kuma su samar da sabbin kudade ga al’ummar jihar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *