Alkalai Sunyi Rantsuwar Da Kadimi Basu Da Hannu A Harkar Ta’addanci A Zamfara

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Alfijr ta rawaito bisa ka’idojin da Gwamnatin Jihar zamfara ta fitar na cewa duk lokacin da zata rantsar da wani wanda ya samu wani mukami a fadin Jihar, dole ne sai an rantsar dashi kan cewa bashi da hannu a har kan ta’addanci dake addabar Jihar.

Bisa ga wannan ka’idojin ne yau jumu’a gwamna Bello Muhammad Matawalle ya umarci alkalin alkalan Jihar Zamfara da ya rantsar dasu.

Rantsuwar ya farune a gidan gwamnatin Jihar zamfara a yammacin yau juma’a, inda kowane alkali da masu bada shawara suka rantse da Alkur’ani Kan Basu taba shiga ko amfani da wani dama da suke dashi ko jin dadin aikin ta’adda dake faruwa a cikin Jihar ba.

Idan ba’a manta ba gwamnan Jihar Zamfara ,Hon Bello Muhammad Matawalle ya fito da wannan tsari na rantsar da mutane wadanda aka baiwa mukamai ne saka makon mawuyacin halin da Jihar ta tsinci kanta man matsalar tsaro kuma aka rika samun wasu masu mukaman gwamnati ko mukaman sarauta da hannu dumu-dumu cikin al’amarin.

Wadanda aka rantsar a Matsayin alkalan manyan kutuna na shari’a, sun haɗa da Alh Abdullahi Muhammad Gusau da Umar Abdul Nasir da
Sa’ad Garba Gurbin Bore da Muttaka
Ahmad Yakub Gusau.

Rantsuwar Kuma ya haɗa da masu bada shawara ga gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle su guda Goma Sha Daya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *