Jam’iyar APC Ta Yi Babban Kamu A Jihar Zamfara

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Alfijr ta rawaito jam’iyar APC a Jihar Zamfara ta yi Babban Kamu, a in da dan takarar kujerar sanatan Zamfara ta Yamma da ’yan takarar majalisar wakilai uku na jam’iyyar NNPP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar ta All Progressives Congress (APC).

Hakan ya gudana ne a Wurin yakin nan zaben gwamnan Jihar a karo biyu da ya gudana a garin Maradun.

Wadanda suka sauya shekar sun hada da dan takarar kujerar Sanatan Zamfara ta yamma na jam’iyyar NNPP, Alhaji Abdul’malik Adamu, mewakiltar mazabar Anka Talata-Mafara da Alhaji Mustapha Na’Allah da shugaban NNPP na karamar hukumar Talata Mafara kuma shugaban kungiyar shuwagaban nin kananan hukumomi na jam’iyar na jiha.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *