Alfijr ta rawaito babban bankin Najeriya CBN ya haramta karbar dala kan hada-hadar kasuwanci a cikin gida yayin da ya kaddamar da shirin nan na kasa da kasa na yin amfani da katin gida na AfriGo.

Gwamnan babban bankin na CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 26 ga watan Janairu, 2023, yayin kaddamar da katin.
Godwin Emefiele ya ce daga yanzu za a biya kudin ciniki a kan dukkan kati a Naira, sai dai na hada-hadar kasuwanci da kasashen waje.
A cewarsa, AfriGo zai kasance mai rahusa kuma zai zama abin alfahari na kasa, tare da yuwuwar bunkasa hada-hadar kudi.
Emefiele ya ce, “Katin gida na kasa yana amfanar mana ikon bayanan mu.
Na biyu kuma, yana zuwa ne a farashi mai rahusa sannan na uku, batun musayar kudaden waje.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇