Alfijr ta rawaito wani aboki ya cakawa Abokin zamansa da suke hayan daki daya tare, kwalba kan kudin wuta da wani makwabcinsu ya bayar.
A yammacin ranar Juma’a ne kakakin ’yan sandan Jihar Delta, DSP Bright Edafe, ta tabbatar mana da faruwar lamarin a yammacin Juma’a, ta kuma tabbatar da kokarinsu na kamo wani wanda ake zargi da hannu a kisan.”
Wannan abun al’ajabi ya faru ne a daren Alhamis a rukunin gidaje na Okumagba Layout da ke Karamar Hukumar Warri ta Kudu a jihar.
Wani ganau ya ce rikicin ya samo asali ne a kan kudin wuta N300 da Oke yake tarawa daga ’yan hayar gidan da suke zama, ya kai wa kamfanin wuta.
A lokacin da ba ya nan ne wani dan haya a gidan ya kawo N300 dinsa ya ba wa abokinsa Allia.
Amma da Oke ya dawo ya bukaci Allia ya ba shi kudin, sai ya ki, wanda hakan ya sa suka fara dambe.
“Da suke damben ne Oke ya dauko wata fasasshiyar kwalba ya caka wa Allia a wuya, jini ya rika kwarara har ya ce ga garinku nan.
Ganin haka sai ya ranta a na kare duba da yadda mutane suka yi kansa suna neman hallaka shi.”
Ya kara da cewa, “Oke ya tsere ne zuwa unguwar Ugborikoko inda aka ’yan sanda suka kama shi.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇