Wasu Ƴan Bindiga Sun Harbe Ɗan Takara A Najeriya

Alfijr ta rawaito ƴan bindiga sun kashe dan takarar jam’iyyar Labour a mazabar karamar hukumar Onuimo a jihar Imo a 2023, Christopher Elehu.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a, 16 ga watan Disamba, 2022.

Baya ga kashe shi, ‘yan bindigar sun kona Gidansa tare da lalata masa kadarori da suka hada da babur.

Wannan na zuwa ne kasa da mako guda, da taron gangamin shugaban kasa na jam’iyyar Labour a Imo.

Wani ganau da bai so a ambaci sunansa ya yi zargin cewa ‘yan bindigar sun kai wa Elehu hari tare da kona kadarorinsa. sun kuma kai hari gidaje da dama tare da harbe-harbe.

Sun raunata da yawa kuma mazauna garin sun yi watsi da su.”

Da yake mayar da martani, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Imo, PPRO, Micheal Abattam, ya ce: “Ana kan bincike kuma rundunar ta tura mutanen mu yankin domin sa ido da kuma sintiri.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *