Alfijr ta rawaito wata mace ‘yar ƙasar Sudan da aka tuhuma da yin zina ta tsallake rijiya da baya daga hukuncin kisa, amma duk da haka za ta yi zaman gidan yari na wata shida bayan ta amsa cewa ta sumbaci wani.
Da farko an yanke wa matashiyar ‘yar shekara 20 hukuncin kisa ta hanyar jefewa, lamarin da ya janyo terere daga ƙasashen duniya.
‘Yan sanda ne suka kama ta bayan kawunta ya kashe saurayinta.
Cibiyar Nazarin Harkokin Shari’ah da Zama Lafiya ta Afirka (ACJPS) ta bayyana hukuncin farko a matsayin wani “gagarumin karan tsaye ga dokar ƙasashen duniya”.
Wata kotu a birnin Kosti cikin jihar White Nile ce ta yanke wa bazawarar hukuncin kisa bayan samun ta da laifin yin zina.
Sai dai bayan taƙaddamar da aka yi ta yi a ƙasashen duniya, kotu ta sake sauraron shari’ar.
Inda daga bisani, alƙalin kotun ya canza tuhumar da aka yi wa matar daga “zina” zuwa wata “baɗala” abin da ke nufin matar za ta yi zaman gidan yari saboda laifin da ta aikata.
Ta dai amsa a kotu cewa ta keɓe da wani mutum kuma ta ce sun sumbaci juna.
Lauyarta Intisar Abdullah ta ce alƙalin “ba shi da zaɓin da ya wuce ya ɗaure ta”.
“Matsalar ita ce ta amsa da bakinta a kotu cewa ta keɓe da namiji, tana cike da ƙuruciya, ba ta san sarƙaƙiyar shari’a irin wannan ba,” lauyar ta faɗa wa BBC.
BBC Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇