Kotu Ta Zartar Da Hukuncin Rataya Kan Wani Jami’in Hisbah

Alfijr ta rawaito Mai shari’a Amina Adamu da ke babar Kotu mai lamba 9 a jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan da ta kama wani tsohon daracta a hukumar Hisbah Dayyabu Muhammad da laifin kashe bazawarsa mai suna Hauwa.

Laifin kisan ya saba doka, ta kundin Pinal Code sashe na 221.

Bincike ya tabbatar da Dayyabu almajiri ne a gidansu Marigayiyar Hauwa, kuma jami’i ne na Hisbah wanda ya nuna sha’awarsa ta auren Hauwa, daga nan suka kulla soyayya.

Yayin da Dayyabu ya zo da maganar aure, iyayen Hauwa sun ce ba za su bashi ita ba saboda suna ganin akwai tangarda a tarbiyyarsa, wannan yasa Hauwa daga baya ta sauya ra’ayi a kansa, tace bata yi.

Wannan lamari dai ya fusata Dayyabu, in da ya zo har gida a shekarar 2011 har daki ya nemi ganin Hauwa.

Bai kasa a guiwa ba nan ya dauko wuka ya caccaka mata a jikinta, kuma wannan dai shi ne sanadin mutuwarta.

Bayan samun gamsassun hujjoji, mai shair’a Amina Adamu ta ce ta gamsu da komai da aka gabatar na hujja, don haka ta yanke masa hukunci ta hanyar rataya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Tags:”YDAN ADAMKANOLABARI

You might like

Previous PostNext Post

Mafi shahara

Ta faru ta kare: Matasa sun yi wa shugaban APC tsirara bayan sun lakada mashi duka a Nasarawa

byIsyaku Garba-December 10, 2022

Yadda shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya mutu ya bar kuyangi 83 – Tsoffin kwamandojin ‘yan ta’adda sun bayyana

December 11, 2022

Saurayi ya yi wa mahaifiyarsa mai shekara 70 dukan tsiya (Bidiyo)

December 14, 2022

Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke tsakanin garuruwa biyu a Najeriya, an rasa rayuka

December 11, 2022

Siyasa

Rukunin labarai

”YANSANDA

ADDINI

AMURKA

AREWA

BIDIYO

BIRNIN-KEBBI

Cuta da maganinsu

DAN ADAM

DUNIYA

ENGLISH

FADAKARWA

Health

ILLOLIN MADIGO

Imam Muhktar Abdullahi

KANJAMAU-HIV

KANO

KASUWA

KATSINA

Kotu jihar Kebbi

LABARI

Mata da suka kashe mijinsu

NISHADI

Politics

Security

SIYASA

Siyasar Kebbi

SOKOTO

TARIHI

TSARO

Yansandan jihar Kebbi

ZAMFARA

ZURU


Adadin mabiya

8597934

Sanarwa

Seniora Tech tana N0.50 Taushi Plaza, Bello way Birnin kebbi. Ita ke tafiyar da shafukan isyaku.com da Seniora News a karkashin kampanin Seniora Int’l Ltd RC 1470216

ABOUT US


Lorem Ipsum is simply dummy text of the printing and typesetting industry. Lorem Ipsum has been the industry’s.

Copyright © 2022 ISYAKU.COM

About

Privacy

Contact Us


Our website uses cookies to improve your experience. Learn more

Accept !

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *