Alfijr ta rawaito hukumar kula da aikin likita ta kasa, ta ce likitocin da su ka samu horo daga kasashen waje akalla 439 ne su ka fadi jarabawar gwajin da za ta ba su damar yin aiki a Nijeriya.
Shugaban hukumar Dr Tijjani Sanusi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce likitocin da su ka samu horo daga kasashen waje 916 ne su ka zana jarabawar, amma 477 ne kawai su ka ci.
Ya ce ana gudanar da irin wannan jarabawar ko ina a fadin duniya, kuma babu wani kwararren da za a bari ya yi aiki a kasar da ba a nan ya yi karatu ba sai idan ya ci jarabawar.
An dai gudanar da jarabawar gwajin ne a asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, domin tabbatar da cewa duk likitan da ya yi karatu a wata kasa ya nuna kan sa a matsayin wanda zai iya gudanar da aikin sa a Nijeriya.
Da wannan lasisin ne, wadanda su ka karanci aikin likita a kowane fannni za su yi aikin wucin-gadi tsawon shekara guda, daga nan ne za a ba su cikakken lasisi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇