Mabiya Kungiyar Shi’a Sun Yi Shiru Kan Rahotannin Mutuwar El-Zakzaky

Alfijr ta rawaito Hukumar kare hakkin bil’adama ta Musulunci (IHRC) ta yi watsi da rahotannin da ke cewa shugaban kungiyar Shi a, a Najeriya, Malam Ibraheem El-Zakzaky ya mutu.

IHRC ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa El-Zakzaky, ya mutu.

Wasu rahotanni da ake ta yaɗa wa sun nuna cewa shugaban kungiyar Shi’ar ya rasu a ranar Litinin.

Sai dai kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta ci gaba da cewa El-Zakzaky yana raye.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, IHRC ta rubuta cewa: “A yau ne ake bukin cika shekara ta 2015 kisan mabiyanta na Zariya.

“Don Allah ku yi watsi da jita-jitar da ake yadawa a safiyar yau cewa Sheikh El-Zakzaky ya rasu.”

A halin da ake ciki, a jiya litinin ne mabiya Shi’a a Najeriya da masu goyon bayansu suka gudanar da bukukuwan cika shekaru 7 da kisan a Zariya.

Ku tuna cewa sojojin Najeriya sun kai hari gidan El-Zakzaky a watan Disamba 2015.

Sojojin Najeriya sun kashe wasu ‘yan Shi’a tare da lalata wurin ibadar El-Zakzay.

Lamarin ya biyo bayan wani hari da ake zargin ‘yan Shi’a ne suka kai wa babban hafsan sojin kasa na lokacin, Laftanar Janar Tukur Buratai a Zariya.

Shaikh Zakzaky da matarsa ​​Zeenat sun rasa ’ya’yansu shida, uku daga cikinsu an kashe su a lokacin Kisan da aka yi a Zariya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *