Alfijr ta rawaito Gwamnan Ribas Nyesom Wike, ya bayyana ra’ayin sa game da makomar Jam’iyyar APC da PDP gabanin zaben 2023.
Wike Yayin ibadar musamman da ta gudana a cocin St. Paul’s Anglican da ke birnin Fatakwal, yace masu Adawa kan tikitin tsayawa takaran jam’iyyar APC Musulmi da Musulmi basuda wata manufa illa arewacin yankin ya cigaba da shugabancin kasar.
A cewar Gwamna Wike, wadanda ke adawa da tikitin addini iri daya yaudarar ‘yan najeriya kawai suke domin har yanzu basuda wata afana face goyon bayan arewa ta ci gaba da mulki a 2023.
Gwamna Wike a cikin wata sanarwa da kakakin sa ya fitar, ya lura cewa irin wadannan mutanen da ke hura wutar suna raina hankalin ‘yan Najeriya ne kawai.
Ya ce: “Kuna wasa da hankalin mutane; kun ce baku yadda ayi takara musulmi da musulmi ba, to shin Najeriya ba ta isa yin tikitin musulmi da musulmi ba ne?.
“Jam’iyyar ku tana son shugabancin kasa ya tafi shiyyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito, ku gaya mana wane ne yake yaudarar to?
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya fito ne daga arewacin Najeriya, daga jihar Adamawa, Haka Iyorchia Ayu shima daga arewacin Najeriya daga jihar Benuwe.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta fada cikin rikici bayan babban taron jam’iyyar da aka gudanar a watan Mayu inda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya doke wasu ‘yan takara 12 da suka hada da gwamna Wike cikin ‘yan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar a zaben 2023.
Gwamna Wike dai bai gamsu da sakamakon zaben fidda gwanin ba, hakan ya sa ke jagorancin ayarin gwamnonin PDP biyar (G5) wadanda ke neman a sauya shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu da dan kudu.
Baya ga Wike, sauran gwamnonin da ke cikin G5 akwai Samuel Ortom (Benue), Ifeanyi Ugwanyi. (Enugu), Okezie Ikpeazu (Abia) da Seyi Makinde (Oyo).
Gwamnonin G5, wadanda aka nada a cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, sun ki amincewa tareda yin biris da tayin da akai musu a Kwamitin yqkin neman zaben shugaban kasar.
A gefe guda rahotanni sun ce Gwamninin na G5 ba su halarci taron gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba, sun kuma ci gaba da kauracewa ayyukan da Atiku da shugabannin jam’iyyar na kasa suka shirya.
Yunkurin sulhunta su har izuwa yanzu yaci tura inda Wike da abokansa ke ci gaba da jan tinga wajan kin shiga yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar ba, yayin da Iyorchia Ayu ke cigaba da rike sitiyarin jam’iyyar PDPn a matakin kasa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Allah sarki aufa su wike rigama sukeyi da arewacin nigeria bawai da atiku kokuma jam iyya suke rigimaba aa mulkinne basaso Dan arewa yakarayi shiyasama amaganarsa yake maganar milki yakara komawa yanki da buhari yafito adamawa arewace danhaka kalu bale akanmu Yan arewa muma inzamuyi kokari muso kanmu to inkuma zamu juyawa namu bayane to bayan xa6e Kuma mufara kar6ar hisabi ahannunmu Allah yaza6a Mana abunda yafi alkhairi sabida annabi muhammad s.a.w.ameen.