Alfijr ta rawaito Wani yaro dan shekara 19 ya dirka wa malamar sa mai shekaru 28 ciki, inda malamar take rokon shi ya taimaka ya aure ta
A lokacin da yaron ya sanar wa mahaifin shi, Richard Nana Sam, cewa yayi da gangan ya zabi mace ta koyar da dan shi saboda bayaso namiji yazo ya dirka wa diyar sa ciki.
Bayan Richard ya wallafa labarin, mutane da dama sun hanzarta zuwa sashin tsokaci, don bashi mafita game da matakin da ya kamata ya dauka
Richard Nana Sam, dan kasar Ghana ne wanda ransa yayi matukar baci, sanadiyyar wani lamari dake wakana a gidan shi, wanda ya yanke shawarar fallasa wa a kafafan sada zumuntar zamani, da sa ran samun mafita.
Yayin bada labarin kalubalen da yake fuskanta a wata sananniyar kungiyar ‘yan Ghana dake da shafi a Facebook, ya kwashe labarin tun daga farko har karshe.
Richard ya bayyana yadda yayi wa yaran shi tagwaye (namiji da mace) masu shekaru 19 hayar malamar da za ta dunga koya musu karatu a gida.
Malamar ta ce, tana dauke da ciki wata uku
Kamar yadda Richard ya fadi, ya tabbatar da bai zabi malami namiji ba, saboda ba zai iya kasadar dawowa gida wata rana yaji labari mara dadi tsakanin mai koya karatun da diyarsa ba.
Amma ga mamakin sa, malamar mai shekaru 28 tazo wurin shi wata rana, ta na shaida mishi labarin abunda yayi kokarin guje mawa.
“Masoya na, bayan wata takwas da ta dauka tana koyar da yara na, wata rana malamar ta zo ta shaida mun tana dauke da cikin yaro na wata uku, inda shi yaron nawa ya amince da lallai cikin nashi ne.
“Ta ce, ta na kaunar yaro na, saboda haka tana so in yarje musu su yi aure,” a cewar Richard.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Tabdi jam