Wani Alkali Ya Rataye Kansa Bayan Ya Kashe Matarsa ​​Tare Da Yiwa Gawar Fyade A Gaban ‘Ya’yansu

.

Alfijr ta rawaito ƴan sanda a Ƙasar Zimbabwe na neman wani alkali ruwa a jallo bisa zargin kisan matarsa ​​kuma ya kashe kansa a wata coci.

Alkalin mai shekaru 36, ya cika wandon sa da iska bayan kisan gillar matar sa mai suna Pholomina Mabika mai shekaru 32.

Rahotanni sun ce alkalin ya shake Phelomina har lahira da hannunsa daga bisani ya yiwa gawarta fyade a gaban ‘ya’yansu,  ‘yar shekara 12 da kuma dan shekara 7.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Zimbabwe, Paul Nyathi ya bayyana cewa “Rundunar ‘yan sandan jamhuriyar Zimbabwe na neman bayanan da ka iya kai ga kama Alkali da ya kashe matar a wani gida dake Cowdray dake gundumar birnin Bulawayo.

“Rahoton yace wanda ake zargin ya kashe matar ta sa, na fama da rikicin aure wanda ya tilasta musu nisantar juna a dakuna daban-daban.

“Bayan kisan gillar da ya yi, wanda ake zargin ya ci gaba dayin lalata da gawar a idon ‘ya’yansa.

Daga nan ne aka gano gawar Alkali Evans Zinzombe a rataye a rufin wani coci dake unguwar Cowdray Park na Bulawayo.

Da take tabbatar da mutuwarsa, rundunar ‘yan sandan kasar cikin wata sanarwa tace “An tsinci gawarsa rataye ne a rufin daki a wata coci.”

Shafin Isyaku

[07/12, 11:35 pm] Musa Best Seller: Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *