
Alfijr ta rawaito Fitacciyar Jarumar Finafinan Hausa wadda aka fi sani da Halima Yusuf Atete, wato Sarauniyar Kannywood na dab da zama Amarya nan da kwanaki.




Za a daura auren Jarumar ne, da Angonta Mohammed Mohammed Kala, a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba 2022, da misalin karfe 10:30am na safe, a Abuja Sheraton Bus Stop, Juma’at Mosque, a garin Maiduguri, da ke Jihar Borno.

Shagalin bikin da za a yi sun hada da :-
Kwallon Kafa,
Margi Day,
Arabian Night,
Dinner.