Labari Mai Dadi: Fursunoni 61 Suka Sauke Alkur’ani Mai Girma A Gidan Gyaran Hali Da Tarbiyya Na Kurmawa A Kano

FB IMG 1783941765174

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali da tarbiyya ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, ta sanar da cewa fursunoni 61 da ke Kurmawa sun kammala sauke Alƙur’ani mai tsarki a wani shiri na gyaran hali da koyar da addinin musulunci.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar a Kano, CSC Musbahu Lawan K/Nassarawa, ya fitar, ya bayyana cewa waɗanda suka kammala sauke Alƙur’anin sun haɗa da maza 55 da mata shida.

Ya kara da cewar, da dama daga cikinsu ba su da cikakken ilimin karatun Alƙur’ani kafin shigarsu gidan gyaran hali, amma sun samu nasarar kammala karatun ne bayan horo da kulawar malamai.

Sanarwar ta ƙara da cewa, domin ƙarfafa musu gwiwa, Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali tare da haɗin gwiwar gidauniyar Chokali Humanitarian Foundation sun rabawa waɗanda suka sauke Alƙur’anin kayan tallafi da suka haɗa da sabbin kaya, katifu, barguna da kuma kuɗaɗen tallafi domin taimaka musu wajen komawa cikin al’umma bayan kammala zamansu.

Mai kula da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Jihar Kano, Ahmed Yusuf Lakpene, ya yabawa babban Kwanturolan Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa jagoranci da goyon bayan da yake bai wa shirye-shiryen ilimi, koyon sana’o’i da gyaran hali a gidajen gyaran hali na faɗin Najeriya.

Alfarma Radio

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *