An gurfanar da wani matashi a gaban kotu bisa zargin dukan mahaifinsa da kuma barazanar kashe shi.

FB IMG 1752685346814

An gurfanar da Ali Hayatu Hotoro a gaban Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba ta ɗaya da ke Kofar Kudu, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Shamsuddin Ado Abdullahi na Unguwar Gini, bisa zargin amfani da ƙarfi da kuma tsoratarwa. Wanda ake tuhuma ya musanta zarge-zargen da ake masa.

A yayin zaman kotun, Alƙalin ya tambayi wanda ake tuhuma ko yana shan miyagun ƙwayoyi. Sai ya amsa cewa ba ya shan ganye, amma yana shan giya. Bayan jin hakan, kotun ta ba da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali.

Ana zargin Ali Hayatu da dukan mahaifinsa tare da yi masa barazanar cewa zai kashe shi. Zarge-zargen ne suka kai ga gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar shari’a.

Daga ƙarshe, kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 3 ga Agusta, 2026, tare da ba da umarnin a kai shi Asibitin Masu Tabin Hankali domin a tantance lafiyar ƙwaƙwalwarsa.

Freedom Radio

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *