Jami’an Hukumar Tsaro ta Ƙasa (DSS) sun kama tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, a safiyar yau Laraba a filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke Enugu.
An kama tsohon ministan ne yayin da ya ke shirin hawa wani jirgin sama mai zaman kansa zuwa Abuja.
Daily Trust ta rawaito cewa majiyoyin tsaro sun ce an kama Nnaji, wanda ya yi murabus daga mukaminsa a watan Oktoban da ya gabata bayan wata cece-kuce, bisa buƙatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) kan zargin yin jabun takardun shaida.
Daga baya DSS ta miƙa shi ga hukumar yaƙi da cin hancin.
A cewar majiyoyin, ICPC ta sha gayyatar tsohon ministan bayan samun koke-koke kan yadda ya gudanar da harkokin ma’aikatarsa, don haka ta nemi taimakon DSS wajen kama shi.
Nnaji ya yi murabus daga matsayin minista a ranar 7 ga Oktoba, 2025, bayan wata yar hatsaniya da ta shafi takardun shaidarsa daga Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) da kuma Hukumar NYSC.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t