Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kalubalanci AVM Ibrahim Umar (ritaya), tsohon Kwamishinan Harkokin Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Musamman, da ya fito ya bayyana irin badakalar da ya zargi Gwamnatin Kano da aikatawa cikin awa 24.
Waiya ya ce idan Umar bai fito ya bayyana hujjojinsa cikin waβadin da aka ba shi ba, to za su fito da abin da suka kira badakalar da ya aikata ta kuΙaΙe a hukumar ayyuka na musamman da ke fadar gwamnatin jihar Kano, da kuma maβaikatar tsaro ta cikin gida da harkoki na musamman, kafin ya bar mukaminsa.
Ya Ζara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bin diddigin dukkan zarge-zarge tare da tabbatar da gaskiya a kan duk abin da aka bayyana.
Don haka kwamishina Waiya ya kara da cewar, tsohon kwamishina AVM Ibrahim Umar, mun baka sa’o’i 24 ka fito da badakalar gwamnati da kace, ko mu mu fito da taka.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan π
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ππ
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t