Bayan Korafe-korafen Al’umma Hukumar Hisba Ta Cafke Wasu Bata Gari A Kanem Suites NNDC Da Sauran Gurare A Kano

IMG 142323 18626 1781789014004

Hukumar hisba ta jihar Kano ta gudanar da wani gagarumin sumame a titin NNDC daura da Yahya Gusau da ke Sharada na Hotel din Kanem Suites da kuma kan titin BUK road da kuma unguwar Danbare tare da kuma layin shisha, bayan wani bayanan sirri da suka samu.

Dr Mujahed Aminudden wanda shine babban mataimakin kwamandan Hisba na jihar Kano ya bayyana cewar an sami nasar kama maza 6, mata 10, ya kuma bayyana cewar dukkanin su basu bata samun su da wannan laifukan ba sai a wannan karon, don haka yanzu suna hukumar ana ja musu kunne, sannan kuma za’a kira iyayen su domin a basu su tare da saka ido akan su har sai sun daidaita sahun su.

A ƙarshen Dr yayi kira ga Iyaye da al’umma kan kara saka ido akan yayansu wajen tarbiyyarsu domin magance shaye shayen miyagun kwayoyi da sauran badala.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *