Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ya bayyana lokacin da ya ke kaddamar da wani kwamiti na mutane bakwai da zai bibiyi yadda ake take dokokin tsara birane da yin gine-gine ba bisa ka’ida ba a jihar.
Sakataren wanda ya wakilci gwamna a waje kaddamar da kwamitin ya ce rashin bin dokokin tsara birane da kula da gine-gine ya zama babban kalubale a jihar kano, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnati na samar da ingantaccen tsarin birane da bunƙasa ababen more rayuwa da kuma kyautata yanayin birnin Kano.
Alhaji Umar Faruk ya ce an kafa kwamitin ne domin gudanar da cikakken bincike kan ayyukan hukumar tsara birane ta (KNUPDA), tare da gano dalilan da ke haddasa ci gaba da take dokokin tsara birane.
Shugaban hukumar KANGIS, Dakta Aliyu Dalhatu Sani ke zamantowa shugaban kwamitin, yayin da Barista Rahma Mallam Alhaji ke matsayin sakatare.
A wani mataki na tabbatar da gaskiya da adalci a binciken, gwamnan ya umarci shugabar hukumar KNUPDA da daraktan sashen zane-zane na hukumar da su ajiye aikinsu na wucin gadi har sai an kammala binciken.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t