Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar tsohon mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu bayan da ‘yan bindiga suka sace shi.
Kwamishinan Harkokin Tsaro da Cikin Gida na jihar, Dakta Nasiru Mu’azu, ne ya tabbatar da rasuwar marigayin cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar da jami’an tsaro suka yi domin ganin an kuɓutar da shi cikin ƙoshin lafiya, lamarin ya ƙare da wannan babban rashi.
A cewar gwamnatin jihar, marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da ciwon sukari da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana rasuwar tsohon janar ɗin a matsayin babban rashi ga iyalansa da jihar Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.
Ya ce lamarin ya sake nuna muhimmancin ƙara haɗa kai wajen yaƙi da matsalar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a ƙasar nan.
Gwamnatin jihar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin tarayya da jami’an tsaro domin ganin an hukunta waɗanda ke da hannu a wannan lamari tare da ƙara ƙaimi wajen magance matsalar rashin tsaro.
Rahotanni sun ce har zuwa lokacin haɗa wannan labari, ba a kai ga karɓo gawar marigayin daga wajen da lamarin ya faru ba.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t