UNICEF Ta Yabawa Gwamnatin Kano Bisa Yin Fice Kan Tallafin Abincin Yara Na Miliyoyin Naira

IMG 20250729 WA0038

Daga Aminu Bala Madobi

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa kasancewarta ta farko a Najeriya da ta bayar da gudunmawar da ya kai Naira miliyan 500 ga asusun samar da abinci mai gina jiki na yara (CNF), inda ta bayyana shi a matsayin gudummawar da ta fi kowacce jiha a kasar nan.

Da take jawabi yayin wani taro wanda yamai da hankali kan kiwon lafiya a Kano, shugabar ofishin UNICEF, Mista Rahama Rihood Mohammed Farah, ta bayyana cewa UNICEF ta ji dadi matuka bisa daidai da kudirin jihar Kano da ta Samar da kudi kusan Naira miliyan 500, wanda ya kawo jimlar tallafin zuwa Naira biliyan 1.

A cewar Farah, an yi amfani da asusun na hadin gwiwa ne wajen sayo katon 12,948 na abincin yara mai gina jiki (RUTF), wanda zai ba da magani ga yara sama da 17,000 da ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki a jihar.

Farah ta lura cewa haɗin gwiwar UNICEF da gwamnatin jihar Kano ya kasance mai ƙarfi kuma yana mai da hankali kan haɓaka sakamakon lafiya da abinci mai gina jiki, musamman ga mata da yara.

Wakilin UNICEF ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya kara saka hannun jari a shirin CNF a shekarar 2025, inda ya ba da tabbacin cewa UNICEF za ta sake ninka duk wata gudunmuwar da za ta bayar domin bunkasa samar da muhimman kayan abinci mai gina jiki kamar RUTF da MMS.

Farah ta kuma bukaci gwamnati da ta tabbatar an gudanar da zagaye na biyu na makon shirin MNCH nan da farkon watan Disamba na shekarar 2025 da kuma samar da isassun allunan da za su iya daukar nauyin yara masu shekaru 12 zuwa 59.

Daganan ta kuma bayar da shawarar a kara biyan kudin hutun haihuwa domin inganta lafiyar mata da jarirai, da karfafa shayar da jarirai nonon uwa zalla, sannan ta yi kira da a fadada ma’aikatan kiwon lafiya a yankunan karkara domin cigaba da hidima ba dare ba rana.

“Kano tayi fice kwarai bisa nuna kyakkyawan jagoranci a fannin kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, da WASH (Ruwa) ta hanyar fitar da kudade akan lokaci, samar da ingantaccen tsare tsare, da samar da yanayi mai kyau da ya dace,” in ji shi.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *