Kotu Ta Daure Wasu Matasa Bisa Samunsu Da Laifin Hadin Kai Wajen Haura Gidajen Mutane

FB IMG 1752685346814

Babbar Kotun Majistare me lamba 24 wadda take zaman ta a Harabar Filin Jirgin Saman Mallam Aminu Kano ta daure Matasan nan biyu Umar Tijjani Mazaunin Unguwar Dorayi Unguwar Bello da kuma Usman Isa wanda aka fi sani da Bawan Allah Mazaunin Unguwar Jaen Layin Dagac.

Kotun ta same su da Laifuffukan Hada baki don aikata laifin Sata da kuma yin barna.

Da yake zartar da hukunci Babban Majistare Muttaka Abba Dandago ya daure Matasan biyu daurin zama a Gidan gyaran hali, kamar haka.

1. Tuhuma ta farko laifin hada baki don aikata laifi Wata uku ko Tarar Naira Dubu 30.

2. Tuhuma ta biyu shiga ta laifi Wata 6, babu zabin tara.

3. Tuhuma ta uku laifin Sata Wata 6 babu zabin tara da kuma wata 2 ko tarar Dubu Ashirin kowannen su.

4. Tuhuma ta hudu laifin aikata barna Daurin wata uku da kuma tarar Dubu 30 ko zaman Gidan gyaran hali na watanni uku.

Kotun kuma ta umarce su da su biya Naira Dubu 75 kowannen su kudin ranko na wayar da aka samu an hannun su kuma sun fasa Gilashin ta ko kuma su yi zaman watanni 10 kowannen su.

Har ila yau Kotun ta hore su da rubuta takardar Alkawari cewa ba zasu sake aikata laifuffuka makamancin wadannan ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *