…Dukannin su tsaffin Shugabannin Najeriya ne ‘Yan Asalin Jihar Katsina.
Daga Aminu Bala Madobi.
Shugaba Alh Umar Yar Adua, Shugaban Kasar Najeriya ne na 13, Wanda yayi fama rashin lafiya alokacin da yake tsaka da Mulki wanda hakan ya gurgunta tafiyar da mulkin sa yadda ya kamata.
Alh. Umar Musa Yar Adua, Goggagen Dan siyasa ne wanda ya jagoranci jihar Katsina a matsayin Gwamna Wanda daga bisani ya zama Shugaban Kasar Najeriya tsakanin 2007 zuwa 2010.
Umar Yar Adua Dan asalin Jihar Katsina ya Shugabanci al’ummar Najeriya Daga watan Mayu 2007-2010.
Yar Adua ya sha fama da ciwon Koda tun kafin ya dare karagar kujerar Shugabancin kasar nan. A 2009 bayan gwaje gwajen likitoci suka tabbatar ya kamu da cutar toshewar hanyoyin jini cikin koda wato (Pericarditis).
A watan Maris 2007, an shilla da Shugaba ‘Yar Adua zuwa Jamus, wanda Mai magana da yawun Shugaban Kasa a lokacin yace ba wani abune ya kai Shugaba ‘Yar Adua zuwa Jamus ba, illa kawai ya je ne domin ya huta saboda gajiya la’akari da aikace aikace na gwamnati a matsayin sa na Shugaba.
Sai dai kuma a ranar 26 ga watan Nuwamba 2009, likitoci suka tabbatar wa Shugaban a dauke da zazzafan ciwon Koda.
A ranar 24 ga watan fabrairu 2010, Y’ar Adua ya dawo Birnin Abuja awani yanayi wanda kusan kowa bai hakikance yanayin da Shugaban ke ciki ba.
Daga karshe a ranar 5 ga watan Mayu 2010 Ƴar Adua ya rasu cikin fadar Shugaban Kasa Dake Aso Rock Villa
Yayi bulaguro zuwa Saudiyyaa watan a ranar 23 ga watan Nuwamba 2009,
‘Yar Adua ya kwashe kimanin kwanaki 109 a bulaguron neman lafiyar sa zuwa kasashen ketare.
A zamanin mulkin sa, A watan Aprilu zuwa watan Augusta 2008, Ƴar Adua a tsaitsaye ya yi tattaki har sau 2 wanda ya kwashe tsawon kwanaki 28 zuwa kasashen Jamus da Saudi Arabia domin neman lafiyar sa.
Hakazalika, a watan Augusta 2009, Tsohon Shugaban Kasa Umar Ƴar Adua ya sake komawa Kasar Saudiyya inda anan ma ya sake kwashe kimanin kwanaki 11.
Daganan, Alkaluma sun tabbatar dacewa tsakanin 2009 zuwa 2010, Alhaji Musa Yar Adua ya sake shillawa zuwa ƙasar Jamus, inda anan kuma ya shafe sama da kwana 70 wanda daga bisani Allah ya yi masa rasuwa.
Saidai rahotonnin kididdiga sun nuna cewa agefe guda Tsohon Shugaban Kasa MUHAMMAD BUHARI shikuma tsakanin 2015 zuwa 2018, ya kwashe kimanin kwanaki 172 a bulaguron neman lafiyar a kasashen duniya.
A watan Mayu 2016, Tsohon Shugaban Kasa MUHAMMAD BUHARI ya garzaya kasar waje domin duba wani addararren ciwon kunne da ya matsa masa, wanda ya lashe kwana 10 likitoci daban daban suna duba shi.
Tsakanin Watan Yuni 2016 zuwa Agusta 2017, yayi bulaguro har sau 3 inda ya kwashe kimanin kwanaki 168 a kasashe daban daban.
Binciken Jaridar Alfijir ya rawaito cewa, Tsohon Shugaban Kasa MUHAMMAD BUHARI ya sake shillawa zuwa Birnin London bayan tattakin dayayi tsakanin watan Yuni 2016 zuwa Agusta 2017, inda ya koma London, inda anan ma ya zauna na tsawon kwanaki 4.
MUHAMMAD ya rasu da misalin karfe 4:30 na maraicen wannan Lahadi a Birnin London bayan fama da doguwar jinya.
An Zabi Shugaban Kasa Buhari Karo Biyu tsakanin 2015 zuwa 2023 karkashin tutar Jam’iyyar APC, Kafin nan ya mulki ƙasar nan a lokacin ya na sanye da kakin Soja tsakanin watan Jinairu 1984 zuwa Agusta 1985.
Tuni Shugaba Tinubu ya bada umarnin sakko da tutar Najeriya kasa-kasa domin nuna girmamawa na nuna alhini kan rasuwar Tsohon Shugaban Kasar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD