Wani jirgin sama mallakin kamfanin Air Peace Airlines ya fuskanci tangarda inda ya kauce daga hanyar tashi (runway) a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa dake, Jihar Ribas, da safiyar Lahadi.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Air Peace, Osifo-Whiskey Efe, an bayyana cewa jirgin ya dan kauce daga hanyar tashi ba tare da wani lahani ba.
A cewarsa, dukkan fasinjojin sun sauka lafiya cikin natsuwa, kuma babu wanda ya samu rauni.
“Air Peace ta tabbatar da cewa jirgi mai lamba P47190, wanda ya taso daga Legas zuwa Fatakwal da safiyar nan, ya fuskanci kaucewa daga hanyar tashi bayan ya sauka lafiya a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa dake Fatakwal.
“Jirgin ya dan kauce daga hanyar tashi ba tare da wani lahani ba. Dukkan fasinjojin sun sauka lafiya cikin kwanciyar hankali, babu wanda ya samu rauni.
“Muna tabbatar wa daukacin jama’ar da ke amfani da jiragenmu da cewa muna nan daram kan alkawarinmu na kiyaye tsauraran ka’idojin tsaro a dukkan ayyukanmu,” in ji Osifo-Whiskey.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD