Kotu ta aike da wani matashi mai saka rigar Mama gidan gyaran hali a Kano

FB IMG 1750349367386

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin mai shari’a Hadiza Muhammad Hassan, ta tura wani matashi mai suna Umar Hisham Fagge, wanda aka fi sani da Tsulange, zuwa gidan yari har zuwa ranar 3 ga watan Yuli, 2025.

An gurfanar da Tsulange ne a gaban kotun, bayan hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta kama shi bisa laifin sanya rigar nono ta mata da kuma tare titi yana yin bidiyon barkwanci, wanda ke ɗauke da abubuwa masu saɓawa tarbiyya da alʼadar al’umma.

Kotun ta tura shi gidan yari, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike da kuma ba da damar duba matakin ladabtarwa.

Hukumar tace fina-finai ta jaddada cewa za ta ci gaba da bin diddigin duk wani abu da ke iya dagula tunanin matasa, musamman masu amfani da kafafen sada zumunta sun sheƙe aya da sunan nishadi.

Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *