Shugaban kungiyar dillalan man fetur ta ƙasa, AROGMA, Alhaji Bashir Dan-Malam ya ce matakin da matatar mai ta Dangote ta dauka na fara rarraba man fetur zuwa ga dillalai a cikin gida Nijeriya ba wani abin fargaba ba ne ga ƴan kasuwar man.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Laraba, Dan-Malam ya ce hasali ma, sayar da man na Dangote a cikin gida Nijeriya zai iya karya farashin kayan a ƙasar.
Ya ce babu wata fargabar durƙusar da dillalan man fetur na Nijeriya da matakin zai yi, inda ya ce matakin sai dai ma ha saukaka tsarin dakon man, wanda hakan zai sa farashin ya ragu tunda a cikin gida za a sari shi ba a waje ba.
“Ba yadda za a yi kace matatar mai ta Dangote ta dinga Hulda da mai mota daya ko mai mota 2, dole masu Depot ne za a zaba a kai musu inda suke, inda masu kanana suje su siya.”.
Sannan ya yi kira ga mambobinsu da su kwantar da hankalinsu domin kungiyar za ta tsaya wajen Kare hakkinsu.
“Za mu zauna da Dangote, za mu tabbatar kowa zai ci gajiyar wannan Abu”.
Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD