Daga Aminu Bala Madobi
Wani Ιan Ζasar Indiya ya gamu da ajalinsa sakamakon ruftawar katangar kamfanin da yake yi wa aiki a kansa.
Ba Indiyen mai suna Harpal Singh yana aiki ne a kamfanin ATCO a anguwar Chikaji da ke karamar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna.
Wani ma’aikacin kamfanin da ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana wa wakilinmu cewa Singh ya gamu da ajalinsa ne a jiya Talata da misalin Ζarfe goma da rabi na dare a lokacin da iskan ruwa ya taso.
Bayanan Da Jaridar Alfijir ta Samu ta rawaito cewa har yanzu ba a san dalilin ruftawar katangar ba, sakamakon lokacin da abin ya faru ba lokacin aiki ba ne kuma ba a san abin da ya kai shi wurin ba.
Duk da cewa kamfanin bai fitar da sanarwa a hukumance ba, yanzu haka gawar marigayin tana dakin ajiye gawa da ke asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya.
Ga Masu Son Bada Talla A Kira +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan π
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ππ
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN