Kwamishina Waiya ya taya Gwamna Abba, Kwankwaso da al’ummar Kano Barka da Sallah
Kwamishinan ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida, ta jihar Kano Com. Ibrahim Abdullahi Waiya ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da Wannan lokaci na bikin sallah wajen yiwa Shugabannin addu’o’in samun nasara gudanar da aiyukan da za su inganta rayuwar al’ummar.
Kwamishina Waiya ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa kuma ya aikewa manema yaɗa labarai
“Wannan lokaci ne mai daraja da na ke rokon Allah madaukakin Sarki ya ci gaba da yi wa mai girma gwamna jagora ya ba shi ikon sauke nauyin al’ummar jihar Kano suka dora masa”.
Ina kuma taya gwamna Abba Kabiru Yusuf da Mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, murnar Barka da Sallah ya Allah ya sake maimaita mana cikin koshin lafiya da kuzari.
Ya ce yana mika gaisuwarsa ta Sallah ga Jagora Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II; da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano da Masu Girma ‘Yan Majalisar Tarayya daga Kano; da kuma abokan aikina masu girma yan majalisar zartarwa ta jihar Kano.
Ga Masu Son Bada Talla A Kira +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇