An hana alkalai da lauyoyi shiga kotuna a Abuja

FB IMG 1747665884023

An hana alkalai da lauyoyi shiga kotuna a Abuja yayin da JUSUN ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani

Alkalan kotu, lauyoyi, ma’aikatan kotu da masu shigar da kara sun kasa shiga hedikwatar Babbar Kotun Tarayya (FHC) da ke Abuja, bayan da mambobin Kungiyar Ma’aikatan Harkokin Shari’a ta Najeriya (JUSUN) suka fara yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Litinin.

An rufe dukkan kofofin shiga cikin harabar kotun da ke kan titin Shehu Shagari, lamarin da ya haddasa tsaiko ga duk wani aiki da ya shafi kotun.

Yajin aikin ya shafi wasu manyan kotuna da ke cikin babban birnin tarayya (FCT), ciki har da Kotun Daukaka Kara da ke Abuja da Babbar Kotun Abuja, inda aka rufe su baki daya.

Daily Nigerian

An fara wannan yajin aiki ne bisa umarnin shugabancin kasa na JUSUN, wanda ya umurci dukkan shugabannin reshe na kungiyar da su tabbatar da cewa mambobi sun zauna a gida tun daga tsakar daren ranar 1 ga Yuni.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *