Gwamnatin Kano ta sanar da  ranar  hutun Babbar Sallah ga makarantun Firamare da Sakandare

FB IMG 1719671782992

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarni ga dukkan makarantun Firamare da na Sakandare a fadin jihar da su tafi hutun Babbar Sallah daga ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025 zuwa Lahadi, 15 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban makarantu kwana, sannan daga ranar Laraba 4 ga Yuni, 2025 zuwa Litinin 16 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban da ke zuwa gida bayan makaranta.

Wani jawabi da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu ya bayyana cewa iyaye da masu kula da ɗaliban makarantun kwana su je su ɗauki ‘ya’yansu da sassafe a ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025.

Sanarwar ta nakalto Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda yana kira ga iyaye da masu kula da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun dawo makaranta a ranar da aka tsara, tare da gode musu bisa goyon baya da hadin kai da suke bai wa ma’aikatar.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *