Dr Gawuna ya zama shugaban hukumar gudanarwar bankin lamunin gidaje a Najeriya

FB IMG 1748523239454

Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, ya karɓi ragamar shugabancin  Hukumar Gudanarwar Bankin Lamunin Gidaje na Ƙasa (Federal Mortgage Bank of Nigeria – FMBN) a hukumance.

A wata sanarwa da Abubakar Musa DK, Mai magana da yawun sa ya fitar, Gawuna ya yi alkawarin tabbatar da gaskiya da amana, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa domin inganta harkokin ci gaba, “wadanda za su ta fi dai dai da  Sabon Shirin nan na (Renewed Hope Agenda) na Gwamnatin Shugaba kasa  Bola Ahmed Tinubu”.

Ya ce, yayin bikin kama aikin, wanda aka gudanar a babban ɗakin taron hukumar da ke birnin Tarayya Abuja, Gawuna ya nuna godiyarsa ga Allah  bisa wannan damar da ya bashi na yiwa ƙasa hidima da kyautata rayuwar al’umma.

“Haka kuma, ya bayyana godiya ga Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu bisa amincewar da ya nuna a gare shi na  naɗa shi a matsayin shugaban hukumar gudanarwa a daidai lokacin da buƙatar samar da gidaje masu rahusa da ci gaban birane mai ɗorewa ke ƙaruwa a fadin kasar nan.

“Ya kuma yabawa Ministan Gidaje da Ci gaban Birane bisa yadda yake kula da al’amuran bankin, tare da jinjinawa  Babban Darakta/Shugaba na Hukumar da sauran manyan jami’an gudanarwa bisa nasarorin da suka cimma a cikin shekara guda, Dr. Gawuna ya bayyana cewa ya na fatan hukumar za ta ɗora bisa wannan nasarori don ganin cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

“Mai Girma Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya ce shugabanci bai tsaya iya muƙami ka dai ba, har ma dai hidimtawa da Kuma kulawa da harkokin al’umma inda ya yi alƙawarin yin koyi da shugabannin baya da suka gina ginshiƙin bankin, tare da yin jagoranci bisa gaskiya da adalci.

Gawuna ya tabbatar da cewa hukumar za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da manyan jami’an gudanarwar don tabbatar da cewa dukkannin shawarwari da za su ƙara ciyar da Bankin gaba musamman a fannin gidaje,x in ji wani ɓangare na sanarwar.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *