Gwamnatin Kano Ta Fara Biyan Naira Biliyan 16 Ga Tsofaffin Kansiloli Da Manyan Ma’aikata

1000057931

Babu gudu ba ja da baya. Babu tsoron magauta. Zamu ci gaba da aiwatar da ayyukan alheri ga al’umma,” in ji shi cikin kwarin gwiwa.

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara biyan haƙƙin tsofaffin kansiloli da wasu manyan ma’aikata da suka yi aiki a kananan hukumomi daban-daban a faɗin jihar.

Wannan biyan da ya kai jimillar Naira biliyan 16 ya gudana ne cikin gidauniyar adalci da mutunta jajircewar waɗanda suka gudanar da aiki a baya.

Gwamna Abba ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da shirin biyan kuɗaɗen da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar ranar Laraba.

“Wannan haƙƙi ne da ya kamata a ce sun dade da karɓa, amma aka tauye su. Mun yanke hukuncin biyansu domin dawo da martaba da adalci,” in ji shi.

Gwamnan ya ce an aiwatar da biyan ne ba tare da la’akari da jam’iyya ko ɓangare ba, yana mai cewa kowanne kansila da ya cancanta zai samu nasa.

Domin sauƙaƙa tsarin biyan, gwamnatin ta raba kuɗin zuwa kashi-kashi:

2014–2017: Kansiloli 903 sun karɓi Naira biliyan 1.8

2018–2020: Kansiloli 1,198 za su karɓi Naira biliyan 5.6 daga watan Yuni zuwa Yuli

2021–2024: Kansiloli 1,371 za su karɓi Naira biliyan 8.2 daga watan Agusta zuwa Nuwamba

Bugu da ƙari, gwamnati ta biya kansilolin da ke ci a yanzu haƙƙokinsu da suka kai Naira biliyan 1.27.

Gwamna Abba ya bukaci waɗanda suka amfana da kuɗin da su yi amfani da su ta hanya mai kyau – wajen bunƙasa sana’o’i, kula da iyali, da tallafa wa al’umma.

“Babu gudu ba ja da baya. Babu tsoron magauta. Zamu ci gaba da aiwatar da ayyukan alheri ga al’umma,” in ji shi cikin kwarin gwiwa.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da zuba jari a fannonin lafiya, ilimi, da samar da jarin dogaro da kai ga matasa.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *